Rigimar Shehu Jaha Da Matar Shi

Wata rana matar Shehu Jaha tayi ta jiransa har cikin dare bai dawo ba. Ranta ya ɓaci sosai saboda kwanakin nan kullum sai sun yi sa-in-sa akan yawonsa na dare.

Tana nan tana ta cika tana batsewa da nufin yau idan Shehu ya dawo ko shi ita.

Shehu jaha kuwa ranar bai dawo ba sai can tsakar dare, Shehu yina tunanin matar tayi bacci don haka ya lallaɓa da nufin ya shige turakarsa.

“Daga gidan wace uwar kake?”

“Laaa! Hajiyata ashe har yanzu baki yi bacci ba?” Shehu ya fada yana murmushin borin kunya.

Matar ta yamutsa fuska tace “ba wannan ne damuwata ba daga ina kake nace?”

Shehu yace “kin tuna da shagon sayar da kayan kwalliyar nan inda kika ga sarƙar zinare kina so? “

Matar Shehu ta washe baki tace “na kuwa tuna”

“Wadda kika ce na saya maki nace bana da kudi a lokacin amma zan saya nan gaba idan na samu kuɗi?”

Matar tace “na gane fa masoyina”

Shehu yace “wallahi shagon na koma na sanya mai shagon ya ɗauko sarƙar nan.”

Cikin farin ciki matar ta rungume Shehu tace “wlh shi yasa baka ɓata man rai kuma kullum soyayyar ka ke ƙara yawa a zuciyata.”

Shehu yace: “bayan an kawo min sarƙar sai na gayawa mai sayar da kayan cewa idan an samu mai sayenta a sayar saboda har yanzu ban samu kuɗi ba.”