Labarai

Rasha Ta Kai Hari Babban Birnin Ukraine, Kyiv Da Jirage Marasa Matuka

A safiyar Lahadi ne sojojin Rasha suka yi amfani da jirage marasa matuka wajen kai hari a Kiev, babban birnin kasar Ukraine.

Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, shaidu sun bayar da rahoton fashewar abubuwa akalla biyar, amma har yanzu ba a tantance iyakar harin ba.

Yayin da ake jin wasu manyan bama-bamai a babban birnin kasar Ukraine, Rasha ta kaddamar da harin jirgin sama a cikin birnin cikin dare.

An ce harin da aka kai da safiyar Lahadi ya dauki tsawon sa’o’i biyu.

A wasu muhimman gundumomi na birnin, ana iya ganin tarkacen jiragen sama marasa matuki suna fadowa.

Har ila yau al’amarin ya yi sanadiyyar lalacewar wasu motoci kamar yadda kafafen yada labaran Ukraine suka bayyana.

Sai dai har yanzu ba a san iyakar harin ba, kuma ba a samu rahotannin farko na jikkatar ba.

A cewar mai magana da yawun sojojin, an kuma yi iƙirarin cewa jiragen sun iso “ƙungiyoyi daga wurare daban-daban”.