Labarai

Ranar Da Aka Kashe Mijina Ya Kira Ni Da Safe Ya Tambayi Lafiya Ta – Zawara

A wata hira da aka yi da Fatima Munir, matar Auwal Abdulsalami, wanda ‘yan ta’adda suka kashe a jihar Imo, ta bayyana tattaunawa ta karshe da mijin ta kafin faruwar lamarin. A cewar ta, A ranar Juma’ar da ta gabata an kashe miji na, ya kira da safe ya tambaye ni lafiya ta

Da take zantawa da Daily Trust, Fatima Munir ta ce, “A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka kashe shi, ya kira ni da safe ya tambaye ni ko na je asibiti domin duba lafiya ta saboda ina da ciki wata bakwai, don haka ya kira ni ya san yanayin lafiya ta.

Na bawa ‘yata wayar, yayi magana da ita ya kuma yi mata alkawarin zai samo mata takalma saboda ‘yata ta rasa takalman makaranta. Bayan sun gama hirar ne na tattara wayar domin yin bankwana, sai kawai na ji an kashe shi a lokacin da yake kokarin gyara wata motar da ta lalace.”

Source: Daily Trust

Advertisement