Olubadan Na Ibadanland Ya Rasu Yana Da Shekaru 93

Olubadan na kasar Ibadan, Oba Saliu Akanmu Adetunji yabi sawun kakanni sa, wato ya rasu.

DAILY POST ta bayyana cewa sarkin ya bi sahun kakanninsa da sanyin safiyar Lahadi.

Sarkin wanda yayi mulki a kananan hukumomi 11 da suka hada da Ibadan, ya rasu ne kasa da wata guda da rasuwar Soun of Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi.

Oba Adetunji ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

Majiyoyi a fadar Popoyemoja na Olubadan sun bayyana cewa Olubadan ya rasu ne a asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta tace, “Eh Olubadan ya rasu.