Neman Suna Ne Yasa Alhaji Sani Ahmad Zangina Ya Kai Ni Kotu – Rarara

Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa shi jogo ne a jam’iyyar All Progressive Congress, APC, amma Alhaji Sani ya kunyata shi a idon manyan mutane da suke ganina da daraja.

Rarara ya kara da cewa, a yanzu haka kullum cikin zulumi muke ni da iyalai na, wannan yasa a yanzu nayi shiru da baki na ba a jina ina cewa komai.