Labarai

Na Harbe Mata Ta Akan Kuskure Bisa Tunanin Mai Garkuwa Da Mutane Ne – Nuhu

A kwanakin baya, Daily Post Nigeria ta ruwaito cewa an kama wani mutum mai suna Nuhu Umar Usman a jihar Bauchi bisa laifin kashe wani dan uwan shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sufeta Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin shi inda ya ce, “Na yi kuskuren harbin mata ta, ta biyu da daddare a tunani na mai garkuwa da mutane ne.

Wanda ake zargin dan shekara 40, wanda ya yi ikirarin lamarin ya faru ne a tsakiyar dare, ya bayyana cewa ya samu sabani da babban dan shi a ranar da ya kori matar shi. Ya yi nuni da cewa, bayan da dan shi ya yi masa barazana, sai ya dauko bindigar shi ta Dawa ya ajiye ta a gefen gadon shi.

Da yake karin bayani, wanda ake zargin ya ce, “Lokacin da tsakar dare ya yi, sai na yi zargin wani motsi a cikin daki na, na yi harbin kan hanyar da za a bi, ban taba sanin mata ta ce ta je yin fitsari tana komawa dakin ba.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya bayyana cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarta.