Na Gaji Da Halin Zinace-Zinacen Mata Ta – Wani Mutum Ya Nemi A Raba Aure Su
Wani dan achaba mai suna Dayo Akingbade ya shaida wa wata kotun gargajita ta Mapo Grade a Ibadan cewa ta raba auren shi da matar shi, Dapo bisa laifin zina.
Da yake mayar da martani game da zargin da matar shi ta yi mai na rashin gaskiya, Akingbade ya yi ikirarin cewa Dapo ba za ta iya shawo kan sha’awar ta ta yin zina ba.
“Alkali, ainihin dalilin da yasa Dapo ta bar gida na shi ne saboda irin rayuwar da ta yi ta zina.
“Bayan an yi ta koke-koke kan yadda take kawo maza daban-daban gida na, mahaifiyar Dapo ta taimaka mata ta kwashe kayan ta daga gida na.
“Jimillar kuɗin da nake samu a kullum Naira 3,000 ne a matsayi na na ɗan Okada, don haka ba zan iya biyan N30,000 alawus na ciyar da yaran kowane wata ba.
“Bayan haka, na sake yin aure tun lokacin da ta bar gida na sama da shekara guda da ta wuce,” in ji Akingbade.
Tun da farko, Dapo, wadda ke sana’ar sayar da kayan kwalliya ta shaida wa kotun cewa ta shigar da karar ne saboda ba ta son ci gaba da zama a matsayin matar shi.
“Bai biyan kudin amaryar aure na ba,” in ji ta.
Da take yanke hukunci, shugabar kotun, Mrs S.M. Akintayo ta ce babu wani auren da za a raba tsakanin mai kara da wanda ake kara saboda rashin sharuddan da ya shafi auren al’ada.
Akintayo ya ce duk wani aure da za a amince da shi a matsayin auren al’ada a karkashin dokokin Najeriya, dole ne a biya kudin amarya (sadaki), da karfin yin aure, ba da kyauta da mika amarya a hukumance.
Ta kara da cewa babu daya daga cikin wadanda aka lissafa a sama a cikin tarayyar Dapo da Akingbade bisa ga shaidar da suka gabatar a lokacin da suke ba da shaida.
Bugu da kari, Akintayo ya baiwa Dap rikon yaran uku da ‘ya’yan biyu suka haifa tare da umurci Akingbade ya biya Naira 30,000 a matsayin alawus na ciyar da yaran duk wata wanda dole ne a rika biyan magatakardar kotu ko kuma kafin karshen kowane wata daga watan Janairu. 2023.
Shugaban kotun ya ba da umarnin hana Akingbade barazana, muzgunawa, cin zarafi da kuma kutsawa cikin sirrin Dapo daga yanzu.
Ta kuma umurci dukkan su da su kasance tare da alhakin kula da ilimi da sauran jin dadin yaran.
Akintayo ya kuma umurci wanda ya shigar da kara da kada ya taba hana wanda ake kara samun damar saduwa da yaran tare da shawarce su da su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.