Mutane 84 Suka Mutu A Harin Tagwayen Bama-bamai – Iran

Hukumomin Iran a ranar Alhamis, sun yi bitar adadin wadanda suka mutu sakamakon tagwayen bama-bamai a kudancin kasar, inda suka ce mutane 84 ne suka mutu.

Fashe-fashen sun faru ne a wani babban taron tunawa da marigayi Janar Soleimani.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na Tehran ya nakalto Ahmad Vahidi ministan harkokin cikin gidan kasar yana cewa “bisa ga kididdigar bincike, an sanar da adadin shahidai 84 ya zuwa yanzu”.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Iran Jafar Miadfar ya tabbatar da adadin wadanda suka mutun da aka yiwa kwaskwarima, wanda ya ce a baya-bayan nan an kashe mutane 95 ne saboda an tsinke wasu gawarwakin kuma an kirga su “sau da yawa”.

A cewar Miadfar, mutane 284 ne suka jikkata sakamakon harin da hukumomi suka yi wa lakabi da “Harin ta’addanci” a kudancin birnin Kerman. Ya kara da cewa “har yanzu 195 na kwance a asibiti”.

Arewa Times Hausa ta bayar da rahoton cewa fashe-fashe a ranar Larabar da ta gabata ya tarwatsa taron jama’ar da ke bikin tunawa da Janar Qasem Soleimani, wanda aka kashe a harin da Amurka ta kai a shekarar 2020 a Bagadaza, Iraqi.

Ko da yake babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, fashe-fashen na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar kan yakin Isra’ila da Hamas da ake yi a Gaza da kuma kisan wani babban jigo na Hamas a kasar Lebanon a ranar Talata.

Wani jami’in Iran ya zargi Isra’ila da Amurka da kai harin. Washington, duk da haka, ta yi watsi da shawarwarin shigar kowace ƙasa.

“Alhakin wannan laifin yana kan gwamnatocin Amurka da Sahayoniya (Isra’ila) ne, kuma ta’addanci kayan aiki ne kawai,” in ji mataimakin shugaban kasar Iran kan harkokin siyasa, Mohammad Jamshidi, a kan X.

Iran ta sha zargin babbar abokiyar gabarta Isra’ila da Amurka da tayar da tarzoma a kasar.

A watan Disamba ne Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyar da aka samu da laifin hada kai da Isra’ila.

Baya ga yakin da ake yi da Isra’ila na dogon lokaci, Iran tana kuma yaki da masu jihadi daban-daban da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka yi ikirarin kai hare-hare a kasar tsawon shekaru.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya zargi “makiya da muggan laifuka” na Jamhuriyar Musulunci da kai harin tare da shan alwashin mayar da martani mai tsanani.