Labarai

Mutane 18 Sun Mutu A Wasu Hare-Haren Ƙunar Bakin Wake A Borno

Akalla mutane 18 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata bayan wasu jerin bama-bamai da wasu ‘yan kunar bakin wake mata suka kai a wani bikin aure da asibiti da kuma jana’iza a jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya.

A ranar Asabar ne wasu bama-bamai uku suka tashi a garin Gwoza da ke kan iyaka daga kasar Kamaru, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Kenneth Daso ya sanar a ranar Lahadi.

A daya daga cikin hare-haren da aka kai da misalin karfe 3:45 na rana (14:45 agogon GMT), wata mata dauke da jariri a bayanta “ta tayar da bama-baman a wani wurin shakatawa na motoci mai cunkoson jama’a”, Daso. ya ce.

An kuma bayar da rahoton cewa, ‘yan kunar bakin waken sun kai hari a wani asibiti da ke garin. Daga baya an sake kai wani hari a wajen jana’izar wadanda fashewar bom din ya rutsa da su, kamar yadda hukumomi suka ce.

“Ya zuwa yanzu, an samu rahoton mutuwar mutane 18 da suka hada da yara, maza, mata da mata masu juna biyu,” in ji shugaban hukumar Barkindo Saidu a cikin wani rahoto.

An kai mutane 19 masu “mummunan rauni” babban birnin yankin Maiduguri, yayin da wasu 23 ke jiran a kwashe su.