Labarai

Murja Kunya Ta Tsere Daga Gidan Yarin Da Take Tsare

An nemi Murja Ibrahim kunya an rasa a gidan yari, tayi ɓatan dabo.

Kasa da kwanaki uku da hukumar hisba ta cafke kuma ta damka murja ga kotu, inda mai Shari’a Nura ya aike da ita gidan gyaran hali

Muna iya cewa an samu labarin ficewar murja daga gidan gyaran halin. Idan zaku iya tunawa dai kotun Shari’ar Musulunci dake zaune a Gama PRP ta aike da murja kunya gidan gyaran hali har sai ranar talata mai zuwa 19/02/2024 za’a dawo domin duba yuwuwar bada beli ko cigaba da shari’a da kuma tsare ta.

Sai dai kuma labarin da muka samu a yanzu Litinin, ya nuna cewa an nema ta an rasa a cikin gidan yarin.