Mun Biya Davido Naira Miliyan N72, Amma Bai Zo Wasan Ba – Pinnick

Tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Amaju Pinnick, ya zargi megastar mawaki, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, da rashin mutunta kwangilar da aka kulla bayan ya karbi dala dubu $94,000, kwatankwacin Naira miliyan N72

Wakilin hukumar ta FIFA ya yi magana a ranar Juma’a yayin taro a karo na 19 a Warri, ya kara da cewa masu shirya gasar sun kuma bada wani jirgin sama mai zaman kansa kan dala dubu $18,000 ga “mai shiryawa da ba a samu ba” amma bai taba zuwa ba.

Ya ce dole ne masu shirya taron suka nemo wani Shallipopi a matsayin wanda zai maye gurbin Davido. Yayi ikirarin cewa ya biya mawakin dala $94,000 kuma ya ba shi kuɗin jirgi dala duba $18,000 domin ya kai shi da tawagarsa a jihar, amma bai zo ba.

A cewarsa, Shallipopi mai ra’ayin mazan jiya dole ne ya shigo domin maye gurbin Davido a matsayin babban taron.

Ya kuma zargi mawakin da girman kai yayin da yake kwatanta shi da abokin hamayyarsa, Burna Boy, wanda ya ce yafi shi nesa ba kusa ba.

“Mun biya Davido dubu $94,600 a ranar 6 ga Afrilu. Mun biya dala dubu $18,000 na jirginsa. Idan ya ce shi babban yaro ne, zamu ce masa mun fi shi girma.”

“Ba wasa nake ba. Don haka, yayin da yake wasannin gaba da baya, mun yanke shawarar farauto wani, Shallipopi don maye gurbinsa.

“Ka ga, lokacin da mutane suka ce suna da girma, ina mamaki. Shin Burna Boy ba shine babban mawaki a Najeriya a yau ba? Burna Boy rabin Itsekiri ne. Kakar mahaifin Burna Boy ita ce Itsekiri. Don haka, ya fi shi girma (Davido).

“Shin akwai wanda ya fi RMD girma a cikin masana’antar wasan kwaikwayo? Ko wanda ya fi Ali Baba girma a harkar barkwanci? Muna da taurari da yawa a Warri. Babu wanda ya kai Warri girma,” in ji shi.