Mohamed Salah Yayi Kiran A Bar Kayan Agaji Su Shiga Gaza

Mohamed Salah ya bukaci kasashen duniya da su taimaka wajen kai kayan agaji a zirin Gaza.

A cikin wani faifan bidiyo da aka saka a kan X, dan wasan kwallon kafa na Liverpool na Masar ya ce “dole ne a bada agajin jin kai ga Gaza nan take.

“Mutanen wurin suna cikin mummunan yanayi. Abubuwan da suka faru a asibitin a daren jiya sun kasance masu ban tsoro. Mutanen Gaza na bukatar abinci da ruwa da magunguna cikin gaggawa,” ya kara da cewa.

“Ina kira ga shugabannin duniya da su taru. Don hana ci gaba da kashe rayukan marasa laifi.”

“Dole ne ɗan adam ya yi nasara.”