Lafiya

Mene Ne Ciwon Sanyin Ƙashi?

Ciwon sanyin ƙashi cuta ce da take samun wani gurbi na zama a tsankanin gabobi, kuma tana yaďuwa cikin sauki zuwa sauran gabobin jiki. Tana kama mutane masu shekaru masu yawa, musamman wanda suke da 55-65. Wasu kuma tana kamasu sanadin infection wato ciwon sanyi.

Abin da keda rikitarwa game da wannan cutar shine, wasu lokuta cutar arthritis, akan zaci cewa URIC ACID ce ko CALCIUM saboda kusan yanayin su yana tafiya kusan ďaya. Amma sai dai ita cutar ARTHRITIS cuta ce mai zaman kanta.

Cutar Arthritis Ta Kasu Kashi Biyu

OSTEOARTHRITIS: Ita tana kama mutane masu shekaru da yawa daga 55 zuwa 65. Alamominta shine, Qashi zaina zafi ko ciwo, ko kumburi. Dadai sauransu.

RHEUMATOID ARTHRITIS: ita kuma cutar sanyice wanda ahausa ake cemata, ciwon sanyin kashi.
Tana farawa ta hanyar jimawan ciwon sanyi ajiki. Tana nuna alama ayayin lokacin damuna, sakamakon danshi.

Wannan atakaice kenan. insha Allahu zamu samu lokaci wajen Karo wasu bayanai akan wannan cuta ta arthritis.