Labarai
Mawaki Rarara Ya Raba Wa Mabukata Kayan Abinci Da N10,000
A daidai lokacin rayuwa ke kara tsanani ga mafi yawancin yan Najeriya saboda hauhawar farashin kayan masarufi, fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya raba wa mabuƙata kayan abinci da kuɗin cefane kimanin Naira dubu N10,000 kowane.
Mun samu labarin cewa Rarara ya bada wannan tallafin a mahaifarsa da ke garin Kahutu ƙaramar hukumar Danja dake cikin jihar Katsina.
Abubuwa dai na na kara hana kansu, musamman kayan abinci ga daukacin yan Najeriya tun bayan gwamnatin ta sanar da kawo karshen tallafin da take bayarwa na man fetur.