Labarai

Matar Da Ta Kashe Mahaifiyarta Ta Miƙa Kanta Ga Hukuma

Wata mata mai shekara 39 wacce ake zargin ta kashe mahaifiyarta ta hanyar ɗirka mata maganin hawan jini fiye da ƙimma ta miƙa kanta ga hukumomin tsaro.

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Yuni, inda matar ta kai kanta ga ofishin ƴan sanda a garin Bengaluru na ƙasar Indiya.

A lokacin da ta isa ofishin, matar mai suna Sonali Sen, ta shaida wa ƴan sanda cewa ita ce ta kashe mahaifiyarta da kanta.

Ta kuma ce mahaifiyarta ta ce ta umurce ta da yin hakan.

A lokacin da ta yi ƙarin bayani kan lamarin, Sonali ta ce bayan ta kashe mahaifiyarta ta sanya gawar a cikin akwati kafin daga bisani ta ɗauko ta ta tunkaro ofishin ƴan sanda.

A lokacin da suka duba, ƴan sanda sun gano hoton mahaifin Sonali a cikin akwatin gawar, wanda ya daɗe da rasuwa.

Ƴan sanda sun ce Sonali ta banka wa tsohuwar ta ƙwayoyin magani hawan jini har guda 30, inda bayan wani ɗan lokaci ta samu bugun zuciya, daga ƙarshe sai Sonali ta yi amfani da wani tsumma ta shaƙe mata wuya, daga nan rai yayi halinsa.

Binciken da ƴan sanda suka gudanar ya nuna cewa marigayiyar ta koma zama a gidan ɗiyarta Sonali da mijinta, waɗanda suke zama tare da uwar mijin.

Sai dai bayanai sun ce tun bayan da ta koma gidan da zama take samu rashin jituwa da uwar mijin ɗiyar tata.

Lamarin yayi ƙamari, inda a ranar Lahadi, toshuwa Biva cikin fushi ta buƙaci ɗiyarta da ta kashe ta.

Yanzu dai ƴan sanda suna tsare da Sonali bisa tuhumar ta da laifin kisan kai, bayan da ta ce ta kashe mahaifiyar tata ce domin cika umarnin da ta ba ta.