Labarai

Matar Da Aka Ɗaure Watanni 18 A Gidan Yari Akan Satar Tukunya Da Zanin Atamfa Ta Samu Ƴanci

Wata budurwa a jihar Adamawa mai suna Ramatu Adamu da ke zaman daurin watanni 18 bisa samun ta da laifin satar tukunya da zani atamfa, ta samu afuwar kwamitin da aka kafa domin rage cunkoso a gidajen yari.

Ramatu, wacce aka yankewa hukunci bisa laifin ‘sata a cikin wani gida’, a ranar Alhamis din da ta gabata ne kwamitin mika gidan yarin Adamawa ya sallame ta.

Kotun majistare dake Numan ta yanke mata hukuncin daurin shekara daya da rabi a watan jiya, 11 ga watan Agusta, bayan da ta same ta da laifin satar tukunyar, nadi da injin sanyaya.

Ta kasance tana hidimar wa’adin ta a Cibiyar Kula da Tsaro ta Numan lokacin da kwamitin ya ziyarci wurin.

Lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin karkashin jagorancin babban alkalin kotun, Mai shari’a Hapsat Abdulrahaman, mai laifin ta ce lallai ta aikata laifin da aka yanke mata.

Ta ce ta bar wurinta a Shelleng ta ziyarci ’yar uwarta a Numan, inda ta kwashe kayayyakin.

Da take amsa rokonta, kwamitin dawo da gidan yarin ya sallame ta tare da gargadi kan duk wani laifi da za a yi.

Alkalin kotun ya kuma ba ta kyautar kudi naira 10,000 domin ta ci gaba da sana’ar sayar da abinci