Labarai

Matar Ali Artwork (Maɗagwal) Ta Haifi Ɗa Namiji

Matar fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Aliyu Muhammad da akafi sani (Ali Artwork) da kuma wani lokaci ake kira maɗagwal ya samu ƙaruwar haihuwa ta ɗa namiji kuma kamar yadda wannan majiysr ta samu labari har an sanya wa yaron suna Muhammad (Aryan).

Ali Artwork dai shine wanda ya fara wallafa labarin a shafin shi na Instagram inda ya yiwa Allah godiya akan wannan ni’ima da yayi mai.