Lafiya

Mace Ta Farko Da Ta Warke Daga Cutar HIV Ta Hanyar Wani Sabon Magani

Ana yiwa wata mata ƴar kasar Amurka maganin cutar na dake karya garkuwar jiki wacce aka fi sani da (Ƙanjamu) ta hanyar kwayoyin jinin da aka yi mata dashen su.

Ƙwayoyin halittar an ɗebo sune daga wani mutum wanda jikin shi yake da kariya daga kwayoyin cuta masu haddasa kamuwa da cutar kanjamau (Ƙabari Salamu Alaikum), a karin maganar Hausawa.

Kawo yanzu dai watanni 14 kenan a jimlace rabon matar da cutar ta kanjamau.

Bugu da ƙari, ƙwararru sun ce hanyar da ake bi wajen yin wannan dashen na kwayoyin halittar da suka hada da jinin da ke wurin cibiya mutum yana da matukar hadari musamman ga yawancin masu dauke da cutar ƙanjamau ɗin.

An bayyana wannan cigaban ne na warkar da matar ne a wani taron kwararrun likitoci a Denver ranar Talata 16 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

Haka zalika, wannan shine karon farko a duniya da aka taɓa sanin cewa an yi amfani da irin wannan hanya domin magance ƙanjamau.