Lafiya

Manyan Fa’idodin Shayin Ganyen Na’a-Na’a 15

Ganyen bishiyar na’a-na’a ganye ne kore mai kamshi da armashi wanda har abinci ake hadawa da shi domin Karin dandano da kuma kamshin abinci.

Ana samun ganyen a kasashen Asia da kasashen Larabawa dama wasu yankuna na nahiyar Afrika.

Bayan samuwar ilmin magunnan musulunci a wasu kasashen musulmai, ganyen na’a-na’a ya samu kar6uwa sosai a cikin jama’a da kasuwannin magunnan Islamic medicine, inda kusan a yanzu nan ne kadai zaka iya samun wannan ganyen a duk jihar da kake zama a Nigeria.

Amfani da ganyen na’a ‘-na’a baya daga cikin magunnan gargajiya,amma kuma masana kimiyar hada magunnan zamani suma sun bada tasu gudummuwa sosai kan alfanon dake kumshe da wannan ganyen,wanda tuni wannan shafin na ciwo da magani ya samu damar zuwa maku da sahihan bayannai dangane da wannan maqala.

Ka nemi busashen ganyen a Islamic medicine store mafi kusa da kai,sai ka nemi ruwa misalin liter daya ka dibi ganyen ka tafasa,idan ya tafasa ka bashi lokaci na akalla mintuna goma,sai ka safke ka tace ruwan da cup karami daidai bukata ka tarfa Zuma cokali biyu manya,ko ka nemi lemun tsami karami ka matse ruwan a ciki ka sha,ko kuma ka sha hakanan ba tareda ka sanya komai ba.kada a saka Lipton, domin Lipton yana daukeda caffeine shi kuma wannan ganyen baya da caffeine a cikin shi.Sai a kula.

1. Yana maganin yawan gas da ya taru a cikin ciki.

2. Yana sassauto kumburin ciki dama rashin jin dadin ciki na ba gaira ba dalili.

3. Idan aka sha shayin na’a na’a, kamin a karya da safe,aka je aka motsa jiki to za a rage qaton tumbi da qiba da kuma nauyin jiki.

4. Idan aka sha bayan an karya to jiki zai samu karfi da kuzari.

5. Idan aka sha shayin a sanda za’a kwanta bacci to za a samu natsuwa da hutu da kuma bacci mai dadi.

6. Idan aka sha bayan da aka ci abinci mai nauyi to zai yi saurin narka wannan abincin har aji ana bukatar a sake cin wani abinci.

7. Idan aka tafasa shayin misalin rabin cup ko liter daya aka tarfa Zuma cokali biyu aka sha da safe bayan an tashi daga bacci to za’a samu kaifin basira da kwakwalwa.

8. Macce mai ciwon ciki da murdawar Mara a lokacin al’ada ta tafasa ta fara sha kwana biyu kamin zuwan al’ada,har kammale. Zata ji dadin jikinta da samun saukin damuwar.

9. Yana maganin tarin mura dama tarin pneumonia domin antibiotic ne mai karfi dake kashin kwayar cuta ta staphylococcus mai haddasa pneumonia din.

10. Maganin warin baki mai fitowa a cikin ciki.

11. Yana maganin ciwon kai na migraine.

12. Yana karawa garkuwar jiki karfi da damar yaqi da kwayoyin cuta dalili da samuwar sinadirin rosmarinic acid a cikin ganyen.

13. Idan aka tirara ganyen a cikin daki yana korar sauro nan take domin sauro baya bukatar jin kashin ganyen.

14. Masu matsalar da ta shafi hormonal imbalance musamman mata to su fake shan shayin na’a na’a.

15. Mai shan wahala a yayin bahaya ga magani a fake sha,za ayiwa Allah godiya domin shi ne mai ciwo mai magani.

Ganyen na’a-na’a shima yana da nashi amfanin mai yawa sosai wurin gyaran fata da sa jiki yayi laushi domin yana da wasu sinadarai masu tsaftace fata.

Yadda Za’a Hada

A samu ganyen na’a-na’a a markada shi, bayan anyi haka, sai a shafe fuska da hannu da kuma jiki, sai a barshi yayi minti goma zuwa sha biyar sannan sai a wanke. Shi wannan ganyen yana kashe kuraje, batar da bakaken tabo dake fuska, da kuma sa laushin fata da kyau.