Lafiya

Magunguna 12 Da Namijin Goro Ke Yiwa Dan Adam

Dafin Maciji

Namijin goro yana kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to a bashi namijin goro guda daya ya ci, insha Allahu nan take zai kashe dafin cizon macijin.

Kashe Maciji

Ana shanya namijin goro ya bushe sai a daka, a barbada a wajen da ba a so macijin ya shiga, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take zai mutu.

Kashe Guba

Duk wanda ya sha wata guba da gan-gan ko bisa kuskure, a basu namijin goro kwara daya ya cinye, insha’Allah zai amayar da gubar da ya sha.

Fitar Da Cututtuka

Ana yayyanka namijin goro a jika a rika sha, insha’Allah duk wata gubar da ke jikin mutum za ta fita.

Karfin Azzakari

Ana cin namijin goro saboda da karin karfi ga masu iyalai ‘yan mintuna kafin a je ga iyalan.

Ciwon Jiki

Cin Namijin goro na magance matsalar ciwon gabobi, kamar yawan gullewa da zugi, yana kuma rage kowane irin radadin azaba.

Maganin Sanyi

Yawan cin namijin goro na kashe kwayoyin cutar da ake dauka wajen saduwa wato STD.

Ciwon Huhu

Cin namijin goro goro na kara lafiyar hunhun dan-Adam.

Garkuwar Jiki

Namijin goro na da kaso mai yawa na sinadarin ‘antioxidant’ Wanda ke da muhimmancin gaske wajen yakar kwayoyin cututtuka da kuma sake gina garkuwar jikin dan-Adam.

Maleriya

Namijin goro rigakafi ne daga kamuwa da zazzabin cizon sauro.

Lafiyar Ido

Cin namijin goro na kare idamu daga makancewa.

Maganin Olsa

Mai wannan larura idan yana cin namijin goro to! insha Allah zai warke.