Lafiya

Maganin Ciwon Yatsa Ɗan Kakare

Ina masu fama da kowanne irin ciwon hannu ko ya kai shekara nawa ne to Insha Allahu cikin ƙanƙanin lokaci zai warke cikin ikon mai sammai da ƙassai.

Idan yi wannan maganin za’a nemi wadannan abubuwa 2 da ke ƙasa:

1 – JIJIYAR TUMFAFIYA
2 – LALLE

Bayan an nemo saiwar TUMFAFIYA sai a bare ɓawon bayan a shanya shi ya bushe, sannan a daka a hada shi da LALLE a daura (Ƙunshi). Insha Allahu kwana daya biyu za asamu waraka daga wannan ciwo.

Kuyi share don ƴan uwa su anfana.