Maganin Ciwon Hanta Na Gargajiya
Duk wanda yake fama da ciwon hanta ya gwada wannan maganin da taimakon Allah za’a dace sosai.
Ka samu albasa guda shida 6 manya sannan ka yayyan ka su kamar za’a yi miya.
Sai a samu ruwa wato misalin galon daya, sai a raba ruwan gida biyu, sai a dauki rabin ruwan sai a dafa albasar.
Bayan na gama dafa albasar, sai a tace albasar a zubar, sannan sai a dauko rabin ruwan da aka ware daban sai a hada shi da rabin daka dafa albasar, sai zama galon guda kenan.
Sai a samu zuma mai kyau, kuma a samu karamin kofi irin na roba ko kuma karamin kofin gilas.
Za’a a rinka cika karamin kofin, sai a dibi zuma cokali uku ka saka a cikin kofin, ana sha sau uku a rana har sai ruwan ya kare da zuman.
Bayan an gama sai a yafi asibiti a yi gwaji Insha Allah za’a samu waraka da yadda Allah.
Allah yasa a dace.