Labarai
Ma’aikaciyar Banki Ta Kashe Kanta Bayan Ta Rubuta Wata Wasika
Hukumomin yan sanda a Najeriya na bincike kan zargin wata ma’aikaciyar banki mai shekaru 32 mai suna Amarachi dake bangaren kasuwanci.
Kafin ma’aikaciyar ta kashe kanta, ta an samu wata wasika da ake zargin ita ce ta rubuta wannan wasika, inda take mai nuna da yanke tsammani game da rayuwar duniya.
A cewarta rayuwar tayi tsanani a Najeriya, ba zata iya jurewa ba, don haka ta zabi barin duniyar, tana mai bawa iyayenta hakurin rasa ta cikin irin wannan yanayi.
Ma’aikaciyar dai ta shiga ban-daki a bankin da take aiki, sannan ta sha guba, kafin daga bisani aka zo aka tarar da gawarta a ban-dakin, a halin yanzu dai ‘yan sanda suna kokarin tabbatar da rubutun hannunta ne a wasikar don gano ko ita ta rubuta da kan ta.