Kungiyar ISWAP Ta Yanke Hannayen Wasu Masunta Bisa Satar Kifi

Rahotanni sun ce mayakan kungiyar ISWAP sun yanke hannayen wasu masunta biyu masu kamun kifi a garin Marte da ke jihar Borno bayan sun zarge su da laifin satar kifi.

An ce masuntan na cikin wata babbar kungiya da ke gudanar da ayyukan kamun kifi a karkashin ISWAP, inda ake biyansu haraji.

Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, wanda ya bayyana hakan ta wani sako a shafin X.
Masuntan biyu sun fuskanci fushin tsagerun ISWAP lokacin da aka same su da rashin biyan haraji.

Zagazola ya kuma ce ‘yan ta’addan sun kwace katanan kifi guda takwas na masuntan.

Ya kara da cewa, mayakan sun bar kwali biyu na kifi dole saboda karancin wurin saka shi, bayan sun dora kifin a kan kwalekwalen su.

Sai dai masuntan sun kwaso kwali biyu da aka yi watsi da su a asirce, wanda ya kai ga ISWAP ta kama su bisa zargin sata.

Bayan kama su, shugaban kungiyar ya ba da umarnin a datse hannayen mutanen kamar yadda shari’a ta tanada.