Kotun Kolin Najeriya Zata Yanke Hukunci Kan Zaɓen Gwamnan Kano Yau

Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano yau Juma’a.

Gwamna Abba Yusuf yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ke Abuja, wacce ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yusuf Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da aka yi ranar 18 ga Maris, 2023.

Kotun kolin ta sanar da ranar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ga dukkan bangarorin da ke cikin karar a ranar Laraba.

Kotun ta bayar da umarnin cewa lauyoyi biyu ne kowanne zai wakilci bangarorin a zaman.

Kwamitin mutane biyar na kotun kolin karkashin jagorancin mai shari’a John Inyang Okoro ya ajiye hukunci kan karar a watan Disambar bara.