Kotu Ta Hana Abauljalil Bayyana Kan Shi A Matsayin Ɗan Abubakar Tafawa Balewa

Babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja ta hana Abuduljalil Balewa yin ikirarin cewa marigayi firaministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa mahaifin shi ne.

Mukhtar, Saddik da Umar, ‘ya’yan marigayi firaministan ne, suka shigar da kara a gaban mai shari’a Peter Kekemeke, suna masu cewa Abduljalil ba dan uwan su ba ne.

Da yake yanke hukunci a kara mai lamba FCT/HC/CV/956/2015, Mista Kekemeke ya ce wadanda suke karar sun tabbatar da karar su. Ya ce sun tabbatar da karar su ne daga shaidun da suka gabatar a gaban kotu.

Alkalin ya ce wanda ake kara, Mista Abduljalil, bai tabbatar da ikirarin da ya yi na cewa marigayi firaminista mahaifin shi ne ba.

“Babu wata shaida da aka gabatar da ta nuna cewa marigayi firaministan mahaifin shi ne ko kuma shaidar inda aka haife shi.

Haka zalika, babu wata shaida da ta nuna cewa an yi aure tsakanin mahaifiyar shi da marigayi Prime Minister. Ni dai ra’ayi na ne masu da’awar sun tabbatar da hujjojin da suka gabatar a gaban kotu,” inji alkalin. “A halin da ake ciki, shari’ar ta yi nasara, an yanke hukunci a kan wanda ake tuhuma a kan wadanda ke kara kamar haka: wanda ake kara bai taba zama dan marigayi firaministan kasar Sir Abubakar Tafawa Balewa ba. An ba da umarnin har abada ga wanda ake tuhuma da ya hana kan shi daga kiran kan shi da ko jika ko dangin Sir Balewa.”

Alkalin ya kara da cewa, “Bugu da kari, neman afuwar jama’a tare da janye duk wani ikirarin da wanda ake tuhuma ya yi a baya a kafafen yada labarai na bugawa da na yanar gizo na cewa shi da ko jikan marigayi firaminista ne. Haka kuma, wanda ake kara ya biya Naira 250,000 a matsayin kudin ikirarin da yayi.”

(NAN)