Lafiya

Ki Guji Yiwa Gaban Ki Wadannan Abubuwa Domin Tsufa Da Lafiyar Farji

Mata su kula da yin wadannan abubuwan mudin suna son su tsufa suna morar halittar su.

Tsarki Da Sabulu

Hakan yasa wasu matan suke amfani da sabulun dake sauya lauyin fata wajen wanke gaban su da shi. Daga bisani kuma su fesawa gaban su turare ko kuma foda.

Duk macen datake yiwa gaban ta hakan, ta sani zata rika jawowa kanta cuta a kullum.

Hakan kuma zai yiwa gaban ta illa inji masana al’uran mata.

Kada ki wanke gaban ki da duk wani sabulun da kika san yanada sinadari mai karfi a cikin shi. Akwai sabulu na musamman da ake sayarwa na wanke gaba na mata.

Idan kuma baki da halin saye, sabulai marasa sinadari masu karfi zasu iya tsaftace gaban mace ba tare da cutar da kanta ba.

Gaban mace baya bukatar a masa feshin turare ko foda, domin wadannan abubuwan suna kunshe ne da sanadarin da zai yiwa mace illa a gaban ta maimakon ya sata kamshi kamar yadda take bukata.

Don haka ki guji fesa turare ko foda a gaban ki domin samawa gaban ki kamshi.

Maimakon hakan kina iya amfani da man zaitun domin shafawa a shatin gaban ki ba a cikin gaban ki ba. Domin cikin gaban ki wannan ruwan shike tsaftace shi ya kuma kare duk wata cuta samun zama a ciki.

Jimawa Da Jikakken Wando

Wasu matan sukan jima da Wandon da sukayi aiki suka yi gumi har gaban su ya jike. Ko kuma suka yi motsa jikin da suka jika gaban su.

Yana da kyau da zaran mace taji wandon dake jikin ta ya jike saboda gumi, ko jikewa da ruwa, tayi maza ta cire wandon domin zama da irin wannan kayan a jikin mace yakan sa ta harbu da infection cikin sauki.

Yawan Shan Zaki

Wasu matan sugar da kansa suke zubawa da yawa idan zasu yi amfani da shi. Haka nan wasu matan kamar sha zumamu suke inada zaki.

Yawan shan zaki ga mace yakan sata tusan gaba kamar yadda masa suka tabbatar. Wanda kwayar cutar fungus candida take haifarwa.

Wannan ya nuna idan mace tana yawan shan zaki gaban ta yana iya kara fadi da girma yadda idan mijin ta na saduwa da ita iska zai rika shiga da fita kamar tusa.

Hakan na ragewa ma’aurata jin dadin Jima’i da kuma kunya ta mace.

Huda Gaba

Akwai matan da suke huda gaban su kamar yadda suke yiwa kunnuwan su, hancinsu da bakunan su domin sakawa gaban su zobe.

Wannan dabi’ar da mata da dama suke yi yakan haifarwa gabansu matsalar kamuwa da cutuka cikin sauki. Bugu da kari kuma fatan wajen ba a yisa domin irin wannan abun ba.

Yana da kyau mata su gujewa huda fatan ganasu domin sawa wajen dankunne.

Akasarin mata ‘yan Madugo da kadan daga cikin wasu matan aure suna sha’awar hakan.

Taba Gaba Da Abu Mai Datti

Muddin mace tana burin ganin ta tsufa da lafiyan farjin ta ta kiyaye taba gaban ta idan hannun ta bai da tsafta, ko kuma amfani da tsumma mara tsafta domin gyara gaban su.

Saka Matsantsun Wanduna

Ki guji amfani da wandon da yake matsai miki gaban ki yadda iska baya samun shigan ki da kyau.

Da zaran kayan sun matsai suna iya jikewa saboda gumi. Wanda wannan gumin zai iya jawo miki shigan cuta a cikin gaban ki. Haka mata masu yawan saka wandunan jeans matsantsun na iya jawo musu matsala.

Shi wannan wajen naki yana bukatar iska a kowani lokaci ba matsi ba.

Turara Gaban Ki

Mata da dama sunada al’adar turara gaban su da hayaki. Wannan dabi’ar ba karamin yiwa gaban mace illa yake yi.

Mata da dama da suke da matsalar bushewar gaba, na rashin ni’ima na faruwa ne a sakamakon raunana sinadarin dake sakon ruwa a gaban mace kamar yadda ya dace.

Gaban mace baiwa yake dashi na tsaftace kansa da kansa da kuna yiwa kansa kariya. Duk wani hayaki da zaki turarawa gaban ki illa ne a wajen ki amma babu wani amfani mai dorewa da zaki samu na aikata hakan.

Yawan Canza Kunzugu

Ki tabbatar da cewa kina yawan sauya kunzugun ki akai akai a lokacin al’adar ki.

Hakan yakan hana cututtuka shigan gaban mace cikin sauki.

Tsangayarmalamtonga

Wadannan wasu abubuwa ne da mata suke yawan aikatasu da suke musu illa a rayuwansu.

Ya kamata mata su fahimci cewa, lafiyan farjin su shine lafiyan zaman Auren su.

Da fatan za a kiyaye.