Kayan Batsa: An Dakatar Da Abdul Saheer, Malam Ali Daga KannyWood

Hukumar Tace Bidiyo ta Jihar Kano ta dakatar da wani jarumin Kannywood, Abdul Saheer, wanda aka fi sani da Malam Ali na shirin nan mai dogon zamgo, Kwana Casain, na tsawon shekaru biyu, bisa samunsa da laifin yin yaɗa kayan batsa a shafukan sada zumunta.

Matakin dai ya biyo bayan zargin da ake yiwa jarumin na cewa yana yada faya-fayen bidiyoyin batsa a shafukan sada zumunta.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Litinin.

Shahararren Jarumin ya shahara sosai a dandalin sada zumunta, musamman TikTok.

El-Mustapha ya bayyana cewa hukumar ta mika goron gayyata ga Abdul Saheer domin ya kare kansa daga zargin yada abubuwan batsa, amma jarumin ya ki amsa gayyatar, lamarin da ya tilastawa hukumar daukar wani kwakkwaran mataki.