Labarai

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Sakawa Sojoji Da Masu Hulɗa Da Su Manyan Takunkumai

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ta kakaba wasu sabbin takunkumai a kan jagororin juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar da mutanen da ke da alaka da su.

Arewa Times ta rawaito cewa takunkumin da aka sanar a ranar Talata ya hada da hana tafiye tafiye da kuma daskare kadarorin da aka yi wa jagororin juyin mulkin da kuma mukarrabansu.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngeale a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar.

Ya ce an yi hakan ne ta hannun babban bankin Najeriya (CBN).

Shi, duk da haka, bai yi cikakken bayani ba.

Tun da farko dai kungiyar ta bai wa shugabannin da suka yi juyin mulkin wa’adin kwanaki bakwai su mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa ko kuma su fuskanci karin takunkumi. Sai dai kuma jagororin juyin mulkin sun ki ja da baya, har ma sun yanke alaka da Najeriya da Togo da Faransa da kuma Amurka.