Labarai

Wani Magidanci Ya Binne Diyar Shi Da Ranta A Dakin Shi

Rahotanni da muke samu daga Jahar Jigawa a arewacin Najeriya sun bayyana cewa wata babbar kotu dake da zama a jahar ta yankewa wani magidanci mai suna Nasiru Hamisu hukuncin kisa bisa samun shi da laifin binne diyar shi yar kimanin shekaru 4 da ran ta a dakin shi.

Babban mai shari’a alkali Ahmed Muhammed Kazaure shine ya yankewa Nasiru Hamisu wannan hukuncin.

Wadanda ke halarce a lokacin yanke hukuncin sun hada mai shigar da kara na yankin, likitan babbar asibitin karamar hukmar mulki ta Ringim Dr. Adamu Musa Aliyu, mai kula da na shari’a na jaha da kuma shaidu gudu uku daga bangaren gwamnati.

Haka zalika iyayen mai laifin sun halarci kotun, uwar yarinyar da aka kashe da kuma tsohowar matar shi Nasiru Hamisu.

Nasiru Hamisu ya aikatan laifin a shekarar da ta gabata 2020, kafin daga bisani yan sanda su kai ga nasarar cafke shi.