Labarai

Jarumin Wasan Kwaikwayo, Samanja ‘Usman Baba Pategi’, Ya Rasu

Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja, fitaccen jarumin wasan kwaikwayo na Hausa, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Tsohon sojan Najeriyar yayi fama da doguwar jinya kuma ya rasu ne sanyin safiyar Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa dake jihar Kaduna.

Samanja kafin ya ja hankalin masu saurare da bajintar sa, ya yi aikin soja sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa a gidan rediyon tarayyar Najeriya (FRCN) da ke Kaduna. Tafiyar sa daga aikin soja zuwa duniyar wasan kwaikwayo ta nuna kyakkyawan aiki da ya sa mutane da yawa suka ƙaunace shi.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya goma sha biyu, ya bar gadon da ya wuce ta fuskar allo. Tasirin Samanja a fagen wasan kwaikwayo na Hausa da irin gudunmawar da ya bayar a fagen soji da watsa shirye-shirye, masoya da abokan aiki za su tuna da shi.