Jarumar KannyWood, Hajiya Binta Ola Ta Rasu

Allah ya yiwa jarumar fina-finan Hausa, KannyWood mai suna Hajiya Binta Ola, Katsina rasuwa.

Hajiya Binta Ola an san ta da tana taka rawa a matsayin maihaifiya a cikin shirin fina-finan KannyWood shekaru da dama.

Ta rasu ne daren ranar Talata 3/10/2023, kuma anyi jana’izar a ranar Laraba 4/10/2023 da misalin karfe 10am na safe, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Allah Ubangiji ya jikan da rahama.