Jami’ar Sojin Saman Najeriya Ta Kashe Kanta A Legas

An tsinci gawar wata mace, Master Warrant Officer a Najeriya, wacce ke aiki a rukunin 651 Base Services Group, ranar Lahadi.

Matar da gidanta ke Block T5 Flat 8 a Sam Ethnan Air Force Base Ikeja, Legas, ta rataye kanta a cikin dakinta da misalin karfe 1400 a ranar 10 ga watan Yuni 2023.

An ce ta rasu ne bayan wasu jami’an soji uku na Air Provost da suka zo tare da wata tawagar jami’an domin kwashe gawar zuwa asibitin sojin saman Najeriya na 661.

Majiyar ta bayyana cewa ba a san musabbabin wannan aika-aika ba, inda ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilin mutuwar ta.