JAMB Ta Sanar Da Ranar Da Za A Yi Rajistar UTME Ta 2022

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta hadin gwiwa (JAMB) ta sanar da ranar 12 ga Fabrairu, 2022, domin fara rijistar jarrabawar kammala manyan makarantu da kuma jarrabawar shiga kai tsaye.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin ya tabbatar da ranar a cikin sanarwar hukumar ta mako-mako da ta fitar a ranar Litinin.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, hukumar ta sanar da cewa “Rijistan UME/DE ta fara ranar 12 ga Fabrairu 2022 kuma ta ƙare 19 ga Maris 2022. Za a yi jarrabawar Mock a ranar 20 ga Afrilu 2022. UTME tana gudana daga 20th zuwa 30th Afrilu 2022”.