IZALA Ta Yi Kira Ga ECOWAS Ta Bi Hanyar Sulhu Maimakon Aiki Da Soja A Nijar
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Kungiyar IZALA tayi kira ga kungiyar ECOWAS da ta bi hanyar sulhu maimakon karfin soji a rikicin jamhuriyar Nijer
Kungiyar wa’azin musulunci ta JIBWIS tayi kira ga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) kan matakin yaki da karfin soji da ta zata dauka akan jamhuriyar Nijer.
Kiran ya fito ne daga bakin Shugaban Izala na tarayyar Naijeriya, kuma shugaban hadin kan kungiyoyin Ahlussunnah na kasashen Afurka Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau a ofishinsa dake sakatariyar kungiyar a birnin tarayyar Naijeriya Abuja.
Sheikh Bala Lau yaci gaba da cewa, yana bada shawara ga kungiyar ECOWAS maimakon a dauki mataki na dawo da shugaba Muhammadu Bazoom da karfin soji, gara a hau teburin sulhu domin hakan yafi alheri, Allah Madaukakin sarki yayi Umarni da a sasanta tsakanin Al’umma kamar yadda yake fada a cikin Suratu Alhujurat ayata 10 cewa; “kawai masu Imani Yan uwan junane, ku sasanta tsakanin yan’uwanku, kuma ku kiyaye ubangiji da hakane za’a tausaya muku”. Kuma “Sulhu Alheri ne” Inji Allah.
Shehin Malamin ya sake bada shawara ga kungiyar ta ECOWAS cewa, Ta zakulo tsoffin ‘yan siyasa kuma dattawa, da Malaman addini da ke yankin Afurka domin a zauna a teburin sulhu a sasanta tsakanin su, tabbas wannan zaifi alheri da taimakon talakawa ga Al’ummar kasar Niger da azo da bakin bindiga inji shi”
Sheikh Bala Lau, ya nemi al’ummar musulmi dake fadin Afurka da su sanya Kasar Nijer a cikin addu’oin su, na Allah ya kiyaye su, ya kare su da bala’in yaki, ya zaunar da kasar Nijer Lafiya.