Isra’ila Ta Kai Wa Ƙasar Iran Hari

Isra’ila ta kai wani hari a cikin kasar Iran, kamar yadda wani jami’in Amurka ya shaidawa CNN a ranar Juma’a, wani abu mai hatsarin gaske a rikicin yankin gabas ta tsakiya da ke ci gaba da kara ruruwa wanda kawo yanzu jami’an gwamnatin Iran suka yi kokarin dakile shi.

Kafofin yada labaran kasar sun sanar da safiyar Juma’a cewa, an kunna tsarin tsaron sararin samaniyar kasar Iran a biranen Isfahan da Tabriz bayan an ji karar fashewar wasu bama-bamai uku a kusa da wani babban sansanin sojin sama kusa da Isfahan.

Manjo Janar Abdolrahim Mousavi babban kwamandan sojojin kasar Iran ya ce fashe-fashen da aka yi a sararin samaniyar birnin Isfahan na da alaka da na’urorin kariya da jiragen sama da suka harbo wani abu da ake tuhuma, wanda bai yi wata barna ba.

Kafar labarai ta Iran, IRNA ta ruwaito cewa wasu jami’an Iran sun ce, sojojin tsaron sama sun kame wasu jirage marasa matuka guda uku kuma babu wani rahoton harin makami mai linzami.

Iran dai har yanzu ba ta gano daga inda aka kawo harin ba.