Isra’ila Ta Cire Sassan Gawarwakin Falasɗinawa 80
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya zargi Isra’ila da satar sassan jikin Falasdinawa 80 da aka dawo da su da sanyin safiyar ranar Talata a mashigar Karam Abu Salem (Kerem Shalom).
Sanarwar ta ce “Ofishin yada labaran yayi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda sojojin mamaya na Isra’ila suka kyamaci mutuncin gawawwakin shahidan mu 80 da Isra’ila ta sace a lokacin yakin da take yi na kisan kare dangi,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan nazartar gawarwakin, a bayyane yake cewa fasalin wadanda aka kashe ya canza sosai a wani mataki na nuni da cewa mamayar Isra’ila ta sace musu muhimman sassan jikinsu.”
Ofishin yada labaran ya ce wannan ba shi ne karon farko da Isra’ila ke “lalata” gawarwakin Falasdinawa ba, kuma ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa na kasa da kasa kan yadda ake daukar gawarwakin Falasdinu da satar sassan jikinsu.
“A baya Isra’ila ta tono kaburbura a Jabalia tare da sace wasu gawarwakin baya ga cewa har yanzu tana da gawarwaki da dama daga zirin Gaza a hannunta,” in ji ofishin.