Isra’ila Da Iran: ‘Yuwar Ɓarkewar Yaƙin Yanki Gaskiya Ne’ – Jordan

Martanin Isra’ila game da hare-haren da Iran ta kai a Isra’ila a makon da ya gabata na iya janyo Gabas ta Tsakiya gaba daya cikin wani mummunan yaki da ke da tasiri a duniya, in ji babban jami’in diflomasiyyar kasar Jordan.

A wata hira da kafar yada labaran kasar ta fitar, ministan harkokin wajen kasar ta Jordan, Ayman Safadi, ya ce kasar shi na zawarcin manyan kasashen duniya kan tabarbarewar lamarin da zai haifar da gagarumin sakamako ga zaman lafiya da tsaro a yankin.

“Hadarin yana da yawa. Hakan na iya jawo duk yankin a cikin yaki, wanda zai yi barna, kuma zai yi matukar tasiri ga sauran kasashen duniya – ciki har da Amurka,” in ji Safadi.

“Al’amarin yana da matukar hadari. Damar rikicewar yankin Gabas Ta Tsakiya na gaske ne, kuma hakan ya kamata ya tsaya. Dole ne mu tabbatar da cewa babu wani karin tashin hankali.” Inji shi.

Majiya: Al Jazeera