Ibrahim Raisi, Shugaban Ƙasar Iran Ya Mutu A Hatsarin Jirgin Sama

Shugaban Iran, Ibrahim Raisi ya mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu yana da shekaru 63.

Tashar talabijin ta CNN ta tabbatar da mutuwarsa, a wani rahoto da kafar yada labaran Iran ta bayar.

A cewar rahoton, ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian shi ma yana cikin wadanda suka mutum tare da wasu mutane bakwai.

Al Jazeera ta ruwaito a baya cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da Raisi ya yi kasa a gwiwa sosai a lokacin da ya ziyarci yankin arewa kuma ba a san halin da yake ciki ba.

Mutuwar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da kazamin fada a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake gwabza yaki a Gaza.

Gwamnatin Iran ta kira wani “taron gaggawa” a ranar Litinin, a cewar kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA.