Hukumar Kwastam Ta Kama Kwantena 20 Na Lalataccen Tumatur Na Miliyan N116

Mukaddashin kwanturolan hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Kwastam), Bashir Adewale Adeniyi, a ranar Juma’a, ya sanar da cewa hukumar ta kama akalla kwantena 20 da ke dauke da tumatur da ya lalace a tashar Tin-Can Island dake jihar Legas.

Shugaban Kwastam, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin kamun, ya lura da cewa, hukumar ta Port and Terminal Multiservice Limited (PTML) na hukumar ta ma’aikatar ne ta kama shi a ranar 8 ga Agusta, 2023 tare da kama wani mutum da ake zargi.

Adeniyi ya yi bayanin cewa tumatur din da ya lalace, wadanda ke da kudin harajin da ake biya (DPV) na Naira miliyan N116, an bayyana su da karya a matsayin suna dauke da harsashi na almond kuma kamfanin Nikecristy Investment Limited ne ya shigo da su.

Shugaban Kwastam din ya lura cewa aikin da ya kai ga kama shi ya yi daidai da manufofin da ya sanya a gaba na Hukumar. Ya kara da cewa manyan manufofin hukumar din su ne dakile fasa-kwauri, kare kudaden shiga na kasa, tabbatar da tsaron kasa, da inganta kasuwanci na halal.

Ya gargadi masu shigo da kayayyaki da su guji shigo da kayayyakin da za su jefa rayuwar ‘yan Najeriya cikin hadari, yana mai cewa kokarin shigar da irin wadannan kayayyakin abinci da ya kare aiki a kasuwannin Najeriya abin takaici ne da rashin uzuri.