Hukumar JAMB Ta Sanar Da Sabuwar Ranar Da Za’a Fara Rajistar UTME

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta sanar da sabon ranar da za a fara rajistar jarrabawar shiga manyan makarantu na bana (UTME) da kuma shiga kai tsaye a kasar nan.

Hukumar JAMB ta sanar da cewa za a fara rajistar UTME na shekarar 2022 a ranar 12 ga Fabrairu.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce a yanzu za a fara rajistar a ranar 19 ga Fabrairu kuma za a kare ranar 26 ga Maris.

Ya ce dage zaben na mako guda shi ne don baiwa hukumar JAMB damar gyara tsarin rajistar masu takara.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Tsarin da za a kammala shi a cikin wa’adin mako guda, shi ma yana da nufin karbar ra’ayoyin ‘yan takara da sauran masu ruwa da tsaki. Hukumar ta yi kira ga jama’a da su lura da shirinta na samar da ayyuka masu inganci ga ‘yan Najeriya.

“Bugu da kari kan abubuwan da ke sama, sabbin hanyoyin inganta rajistar UTME na 2022 za a samar da su a gidan yanar gizon hukumar, tallar ta na mako-mako da sauran kafafen yada labarai a ranar Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022.”