Haren-Haren Isra’ila Sun Lalata Masallatai 380 A Gaza

A cewar wata sanarwa da ofishin yada labaran Gaza ya fitar, masallatai akalla 380 aka lalata – ciki har da tsofaffi masu shekaru sama da 1,000.

Rugujewar wadannan masallatai ya haifar da bacewar kiran salla daga unguwanni da dama a yankin Zirin Gaza, da kuma dakatar da kararrawar majami’u.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, an lalata majami’u uku a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai.

Ofishin yada labarai na kira ga kungiyoyin addini na duniya da su yi Allah wadai da lalata wadannan wuraren ibada.