Hanyar Da Za’a Magance Matsalar Kurajen Fuska Da Sauri
Kurajen fuska, wato (Pimples) a turance, cuta ce ta fata gama gari wacce take shafar kimanin kashi 85% na mutane a wani lokaci a rayuwarsu.
Cutukan sun hada da kuraje masu kaikayi wadanda zasu iya zama masu takaici da wuyar warkewa.
Haka nan, mutane da yawa sun juya zuwa wasu hanyoyin na gida don kawar da pimples da sauri, yayin da akwai magungunan cututtukan fata da yawa a ko ina, ƙalilan ne kawai aka tabbatar cikin ilimin kimiyya na taimakawa wajen maganin kurajen.
Anan akwai hanyoyi da dama na yau da kullun don kawar da pimples da sauri.
Yanda Za’a Yi Maganin Pimples;
Koda yaka akwai wadansu magunguna na gargajiya daban-daban akan wannan matsalar, amma kuma wadansu kayan hade-haden suna da wahalar samau ga wasu mutanen. Saboda haka zamu kawo muku hanya mai sauki anan wacce a ko ina za’a samun su;
1. Za’ a samu wani magani da ake kira “Aspirin”, shi maganin na asibiti ne, wato kwayoyi ne. Idan an samo “Aspirin” din sai a maida shi garri, ma’ana a nike shi.
2. Idan an maida “Aspirin” gari sai a samu man “Zaitun” wato “Olive Oil” da kuma “Ruwan Khal”, sai su ruwan da man ana samun ne a wuraren sai magunguna na musulunci, ma’ana islamic medicine centre.
3. Sai a hada wadannan ababen da muka ambata wajen daya, gwargwadon yan ake son yawan na su, sai a juya har su kade sosai, sai a rika shafawa a inda kurajen suke.
4. Wannan hadin yana maganin dukkanin wani rashin lafiya da ya shafi fatar dan adam baki dayan ta.
Gargadi: Sannan kuma a daina matsa pimples din domin matsar zata iya sanya su fito sosai kuma suyi wuyar magani, wani lokacin sukan tsananta.
Domin neman karin bayani game abinda muka bayyana a cikin wannan matsalar sai a tuntube mu akan wadannan emails; Info@arewatimes.com.ng ko uai4466@gmail.com.