Gwamnatin Sojan Nijar Ta Umarci Ƴan Sanda Su Kori Jakadan Faransa
Rundunar sojan Nijar ta soke kariyar jakadan Faransa tare da umurtar ‘yan sanda da su kore shi daga kasar da ke yammacin Afirka, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin mulkin soja.
Sojojin da suka hambarar da shugaban Nijar sama da wata guda sun ba jakadan Faransa Sylvain Itte sa’o’i 48 ya fice daga kasar a makon jiya. Wa’adin ya kare ne a ranar 28 ga watan Agusta ba tare da Faransa ta kira Itte ba.
Gwamnatin Faransa ta ce ba ta amince da masu yunkurin juyin mulkin a matsayin halastattun shugabannin kasar ba, kuma mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Faransa Anne-Claire Legendre ta fada jiya Alhamis cewa jakadan yana nan a wurin duk da barazanar korar da ake yi.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta aike a farkon wannan makon kuma kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya gani a ranar Alhamis ta ce Itte “ba ya samun gata da kuma kariya daga matsayinsa na ma’aikacin diflomasiyya na ofishin jakadancin.”