Gwamnatin Neja Ta Haramta Jigilar Kayan Abinci Da Manyan Motoci Zuwa Sauran Jihohi
Gwamna Mohammed Bago na jihar Neja ya hana sayarwa da raba kayan abinci da amfanin gona da yawa wanda ake dauka da manyan motoci daga jihar zuwa wasu jihohin Najeriya.
Bago ya sanar da dakatarwar ne a yayin ganawa da manema labarai, inda ya jaddada cewa sayar da kayan abinci da yawa zuwa wasu jihohi ya haifar da karancin abincin da yunwa a jihar.
Gwamnan ya ce, “Motoci masu zuwa yin kaya ko siyan kayan abinci da yawa daga mutanen garin mu ya kamata a dakatar da su a yanzu. Mun dakatar da saye-sayen kayan abincin daga kasuwannin kananan hukumominmu, da karkara daga yanzu.
“Duk wanda aka samu yana yin haka, mun baiwa wasu jami’an tsaro su ci gaba da kwace wadannan motocin tare da raba abincin ga jama’a.”
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsalar tattalin arziki.
Sakamakon faduwar darajar Naira, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a fadin kasar, wanda hakan ya janyo wahalhalu.