Labarai
Gwamnatin Kano Ta Ware Miliyan N854 Ga Shirin “Auren Zawarawa”
Gwamnatin jihar Kano ta amince da Naira miliyan 854 ga Auren Zaurawa (Mass Wedding Initiative) da kuma miliyan N700 don biyan kudin makaranta ga ‘yan asalin jihar Kano 7,000 da ke karatu a Jami’ar Bayero Kano (BUK).
An amince da hakan ne a ranar Laraba a taron majalisar zartarwa na jihar saboda matsalar tattalin arzikin kasar.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis ta hanyar sa na X, wanda aka fi sani da Twitter.
Ya rubuta: “Haka kuma daga taron na jiya. Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da fitar da zunzurutun kudi har naira miliyan N854 na kashi na farko na shirin bikin aure na Auren Zaurawa.
“Da kuma Naira Miliyan N700 na kudin karatu na dalibai 7000 na Jami’ar Bayero Kano (BUK).”