Gobarar Tankar Man Fetur Ta Kashe Mutane 74 A Laberiya

Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar wata tankar mai a tsakiyar Laberiya ya kai 74, in ji babban jami’in kula da lafiya na kasar dake Afirka ta Yamma a ranar Litinin.

Wannan sabon adadi ya karu sosai kan adadin mutane 40 da suka mutu a baya sakamakon bala’in na ranar 26 ga Disamba.

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasar George Weah ya ayyana zaman makoki na kasa ga wadanda abin ya shafa da kuma iyalansu.

Babban jami’in kula da lafiya na Laberiya Francis Kateh, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, adadin wadanda suka mutu a halin yanzu sun haura 70.

Ya kara da cewa “Akwai wasu da suka koma toka, don haka har zuwa yanzu, muna kokarin gano adadin,” in ji shi.

Ya bayyana a cikin sakon da ya aike daga baya cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 74.

Shaidu sun ce mutane sun hau motar ne domin kokarin tattara man da ke kwarara daga tankinta bayan da ya fado ya fada cikin wani rami da ke kan hanyar Totota mai tazarar kilomita 130 daga Monrovia babban birnin kasar.

Wani mazaunin yankin Aaron Massaquoi ya shaidawa AFP a lokacin cewa “wasu mutane sun hau kan tankin domin samun mai. Wasu daga cikinsu suna da sandunan ƙarfe suna bugun tankar don ta fashe domin ɗibar man fetur ɗin”.

Kimanin mutane 40 ne suka mutu nan take sakamakon fashewar tankar da wuta, yayin da wasu kuma aka kai asibiti domin yi musu magani, da dama daga cikin su sun mutu a can sakamakon raunukan da suka samu.

Jami’ar kula da lafiya a yankin Cynthia Blapooh ta shaidawa Front Page Africa cewa wadanda abin ya shafa sun hada da yara da akalla mace mai juna biyu.

Laberiya ita ce kasa ta 10 mafi talauci a duniya, inda fiye da rabin al’ummarta miliyan biyar ke fama da matsanancin talauci.

Weah, tsohon dan wasan kwallon kafa da ya dare kan karagar mulki tun a shekarar 2018, zai mika ragamar mulki a ranar 22 ga watan Janairu ga Joseph Boakai bayan shan kaye da ya sha a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a watan Nuwamba.