Gobara A Harabar Kotun Kolin Najeriya

Akwai rahotannin gobara a harabar kotun kolin.

Ana zargin an kona ofisoshin alkalai uku.

Rahotanni sun bayyana cewa Dr. Festus Akande, daraktan yada labarai na kotun kolin Najeriya ya tabbatar da faruwar gobarar.

“An kashe gobarar daga baya, ba a samu asarar rai ba, a cewar Akande.

Rahotanni sun nuna cewa wutar lantarki ce ta yi sanadiyyar tashin gobarar.

Jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya sun kashe gobarar, kuma komai ya koma dai-dai, kamar yadda jaridar DAILY POST ma ta gano.