Labarai

Fitar Nijar ECOWAS: Abin Sani Game Da Wannan Mataki

Kasashen yammacin Afirka uku karkashin jagorancin soji sun sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS cikin gaggawa, suna masu zargin kungiyar da zama barazana ga mambobinta.

Kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun yanke shawarar ficewar kasar daga kungiyar ECOWAS cikin gaggawa.

ECOWAS “karkashin tasirin kasashen waje, cin amanar ka’idojin da aka kafa ta, ya zama barazana ga kasashe mambobinta da al’ummarta”, in ji sanarwar.

Kasashen uku sun zargi kungiyar ta yankin da gazawa wajen tallafawa yakin da suke yi da “ta’addanci da rashin tsaro”, tare da sanya takunkumin karya doka, da rashin bin doka da oda da kuma rashin da’a.

Martanin ECOWAS

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta ECOWAS ta fitar ta ce ba a sanar da ita matakin da kasashen suka dauka na ficewa daga kungiyar ba. Yarjejeniyar ta ta tanadi cewa janyewar yana ɗaukar har zuwa shekara guda kafin a kammala.

Abin Lura A Fita Kungiyar

A duk lokacin da aka ce kasa ta fita ƙungiya irin haka, kafin mu yi yabo ko suka, kamata yayi mu fara nazarin meye zai kasance sakamakon wannan fita kungiyar.

Babban ma’aunin awon ka shi ne wane hali al’ummar wannan kasashen za su shiga, idan na ce al’umma ina nufin talakawa wadanda su ne su ka fi yawa. Kar ka auna da maganganun masu rubutu ko masu shiga gidajen talabijin domin mafi yawancin su gwamnati su ke yiwa aiki.

Mu dan duba, kamar yadda wasu ke cewa idan dan Nigeria zai shi ga Niger sai yayi visa a yanzu, to su kuma yan Niger, Mali ko Burkina Faso idan zasu shigo Najeriya fa?

Adadin yan Niger da ke kasuwanci da sauran ayyuka na neman kudi a Nigeria, Cameroon, Ivory coast, Ghana da sauran su, ya makomar su za ta kasance?

Idan yanzu Najeriya da sauran ƙasashen ECOWAS su ka ce zasu kore duk yan Nijar su mayar da su kasar su, ita ma Nijar ta kore na su, ya kake tunanin kuncin da zasu shiga?

Wane karfin tattalin arziki Nijar ko sauran ƙasashen suke da shi da zasu iya daurewa ba tare da hulda da wadannan manyan kasashe na Afrika ba ta hanyar da al’ummar su ba zasu shiga matsin rayuwa ba?