Labarai

FIFA Ta Dakatar Da Shugaban Kwallon Ƙafa Na Sifaniya

Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya dakatar da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Spain Luis Rubiales na tsawon kwanaki 90 bayan da ya kama kan ‘yar wasa Jenni Hermoso tare da sumbatar ta a lebe bayan nasarar da Spain ta samu a gasar cin kofin duniya ta mata.

A ranar Juma’a ne ake sa ran Rubiales zai sanar da murabus din nasa amma a maimakon haka ya ce ba zai sauka ba kuma RFEF ta yi barazanar daukar matakin shari’a na kare shi bayan Hermoso ta ce ba ta amince da sumbatar da ya yi mata ba.